Sakonnin Masu Karatu (2017) (5)

Ci gaban sakonnin masu karatu.  A sha karatu lafiya.

148

Assalamu alaikum Baban Sadik bayan dubun gaisuwa da fatan alhairi da fatan kana cikin koshin lafiya. Don girman Allah kataimaka ka turo mini kasidar Titanic ta wannan Imel:  sirajoh2@gmail.com.  Na gode Allah ya kara basira amin.

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Sirajo.  Ka duba akwatin Imel dinka, tuni na cilla maka kasidar.  Allah amfanar damu baki daya, amin.  Na gode.


Assalamu alaikum. Don Allah yawan masu sauraron tashar rediyo daya a lokaci guda, ya kan jawo mata cunkoso ne?  Kuma tashar da ake sauraro suna gane yawan masu sauraro?  Na gode. Daga Yahaya Lawan Abubakar, Nassarawa, Kano Nijeriya

Wa alaikumus salam, barka ka dai Malam Yahya.  Ba yawaitan masu saurare bane ke sanya samuwar cunkoso da cushewar ingancin sauti a tashar rediyo ba, ko kusa.  Abin da ke haddasa rugugin da kake ji shi ne samuwar tsaiko sanadiyyar abubuwan da sakonnin sautin rediyon ke cin karo dasu a sararin samaniya kafin isowa akwatin rediyonka.  Idan na’urar daukan shirye-shiryen rediyo mai suna “Receiver” ta dauki sauti daga dakin shirye-shirye, takan cilla shi sama ne, yabi titin sadarwa dake sararin samaniya.  Yayin wannan shawagi ne kafin isowarsa akwatunan rediyonmu, idan yaci karo da wani sakon, ko kuma aka samu hatsaniya na isa ko ruwan sama, ko kuma wayoyi masu dauke da makamashin lantarki, sai kaji wannan rugugi.  Wadannan abubuwa da sakon sauti ke cin karo dasu a hanyar tafiyarsa, su ake kira: “Noise” a fannin sadarwar zamani.  Da fatan ka gamsu.


Assalamu alaikum Baban Sadik sunana Engr Mohammed Abba.  Ina zaune ne a jihar Yobe. Ina sana’an gyaran waya.  A kullum burina inaso in kirkiri wani abu wanda kasata za tayi alfahari kuma taci gaba.  Amma sai ga shi iyayena masu kananan karfine, shi ne a kullum ina hawa Intanet saboda ko zan samu mai irin tunanina a harkar kimiya da fasaha.  Dan Allah kaban shawara Baban Sadik; wace hanya zanbi?  Na gode: 08037714434

Wa alaikumus salam, barka ka dai.  Da fatan kana lafiya.  Da farko ina mai baka hakuri sanadiyyar lokacin da na dauka kafin baka amsa.  Ina sane da wannan sako nake tuni.  Abu na biyu shi ne, kasancewar iyayenka ba masu hali bane bazai zama dalilin gazawarka wajen samar wa al’umma abin da za su dogara ko amafana dashi ba, a bangaren kimiyyar kere-kere.  Shi cin nasara a rayuwa ba ya ta’allaka ga kudi: yana ta’allaka ne ga jajircewarka wajen kokarin cinma manufarka, da dagewarka wajen neman abin da zai kaika ga gaci, da kuma hakuri na tsawon zamani kana bugawa.  Abu na karshe da zai tabbatar maka da muradinka kuma shi ne kaddarar Allah; idan Allah ya kaddara maka yiwuwar abin, sai ya yiwu.  Idan kuma ba ya cikin abin da Allah ya kaddara maka a rayuwarka, komai tarin dukiyarka ko na iyayenka, haka za ka hakura da abin da kake so.

Shawarar da zan baka, kamar yadda na baiwa wadanda suka gabaceka ita ce: na farko, ka tsara abin da kake son cin mawa, na buri.  Ma’ana, me kake son ka kawo cikin al’ummarka na ci gaba?  Idan ka gama tantance wannan, sai abu na gaba, wato hanyoyin da za ka bi wajen aiwatarwa.  Wannan shi ne matakin da yafi kowannen tsauri kuma yafi bukatar juriya da jajircewa.  Akwai cibiyoyi da gwamnatin tarayya da jihohi suka tanada karkashin tsare-tsaren samar da sana’o’i inda kuma ake koyar da nau’ukan ayyukan yi daban-daban.  A ire-iren wadannan wurare kana iya inganta sana’arka ta gyaran waya, ko ma, idan tayi nisa a dauke ka a matsayin mai karantar da dalibai wannan sana’a mai mahimmanci.  Idan kuma kana son canza sana’a ne, duk a ire-iren wadannan cibiyoyi kana iya zaban wanda kafi sha’awa.

- Adv -

A karshe ina maka fatan alheri, Allah albarkaci rayuwarka a duk inda kake, amin.


Assalamu alaikum Baban sadik, barka da warhaka, da fatan kana lafiya. Tambayata ita ce: wai don Allah ya ya ake bude shafin gidan yanar sadarwa a waya?. Allah ya kara basira, amin. Na gode: abdulraufabubakar588@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai.  Duk da cewa ban san nau’in wayar da kake amfani da ita ba, amma ko ma wace iri ce, idan ka budo “Menu” za ka ga “browser” mai suna: “Web” ko “Internet” ko “Opera”, ya danganci nau’in wayar.  Sai ka budo, da zarar ka budo nan take za a kaika shafin farko.  Amma kafin nan, ka tabbata ka bude “Data” din wayarka, domin idan baka bude ba, ko kuma ka bude amma babu “Data”, za a ce maka: “Shafin da ka bukata ba ya nan”, cikin harshen turanci.  Da zarar shafin ya budo, sai ka latsa filin dake saman shafin, inda adireshi yake kenan, wato: “Address Bar,” zai canza launi zuwa launin shudi, alamar cewa kana iya shigar da rubutu a ciki kenan.  Daga nan sai ka rubutu adireshin shafin da kake son hawa.  Misali, idan labaru kake son karantawa kana iya ziyartar shafin Daily Trust dake: www.dailytrust.com.ng, nan take za a budo maka shafin kai tsaye.  Da fatan ka gamsu.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum, don Allah a turo mini da bayanin hanyoyin da zan fara koyon ilimin kwamfuta tare da wasu mukalolin da ka rubuta akan kwamfuta, dan Allah.  Daga Usman Aliyu Abdussalam: kunduntarihi@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Aiyu.  Kamar yadda na fada makonni biyu da suka gabata, tuni n agama bayani kan wannan maudu’i, don haka sai ka duba akwatin Imel dinka, na tunkudo maka abin da ya sawwaka.  Allah sa a dace, amin.


Assalamu alaikum Baban Sadik, mene ne yasa ake kiran Chales Barbage da lakabin “Baban Kwamfuta”, wato “The Father of Computer?”  Nasiru Kainuwa Hadejia 08100229688: knw6339@gmail.com

Wa alaikumus salam, barka dai Malam Nasiru Kainuwa Bahadeje.  Dalilin da yasa ake kiransa da lakabin “Baban Kwamfuta” shi ne, don a duk cikin wadanda suka kirkiri abubuwan da a yanzu ake kididdige su a tarihin kwamfuta wajen samuwa da asali, shi ne ya kirkiri na’urar da ke da siffofin da kwamfutocin zamanin yau suka gada, wadanda kuma suka basu kama da kimar da a yau ake alfahari dasu.  Wadannan siffofi kuwa su ne, karban umarni daga maginin manhajar kwamfuta (Programmer), don aiwatr da umarnin nan take, da kuma tsarin karban bayanai a matsayin sifili da daya (0s and 1s).   Wadannan su ne manyan siffofin kwamfutocin zaman yau, kuma su ake kira: “Digital Programmable Computers.”  Wannan shi ne babban dalilin da yasa aka masa wannan lakabi.  Da fatan ka gamsu.

- Adv -

You might also like
2 Comments
  1. Abdulmalik hassan danmoyi says

    Asslm baban Sadik don Allah katuro man yadda zanyi infara lekin Asiri da Waya ta kirar android v4.2.2 ta gmail dina kuma wlh ba cuta zanyuba Allah sheda don allah katuroman yau nogode Daga abdulmalik Hassan danmoyi. imail danmoyihassan@gmail.com Allah ya arbakaci rayuwar Sadik

  2. bashir chika yaro says

    assalamu alaikum baban sadik muna godiya da irin iliminda kake sanaddamu baban sadik ni kafintane ina buga kujeru cushion kuma alhamdu lillahi gwargwado nakware fannin kujerun har ina kirkiradda kujerunda babusu don allah wace hanya zanbi tayadda zaasandani musamman nahiyar turawa ina neman shawararka nagode akoda yaushe munayimaka fatan alhairi nagode allah yakara maka ilimi da lafiya dagamawa lafiya ameen.

Leave A Reply

Your email address will not be published.