Tallafin Fasahar Hasken “Laser” Ga Fannin Likitanci (1)

Daga cikin nau’ukan fasahan dake amfani da haske akwai “Laser Light”, wanda a halin yanzu ake amfani da ita hatta a fannin likitanci. Wannan shi ne abin da za mu duba a wannan mako.

574

Matashiya

Watanni uku da suka gabata wani direba ya kamu da ciwon ido mai tsanani, inda har ya wayi gari ba ya iya tukin mota sai dai a tuka shi.  Wannan abu ya ci masa tuwo a kwarya musamman lokacin da likita ya sanar da shi cewa sai an masa tiyata a saman giran idanunsa, don magance wannan matsala.  Daga nan kuma wata sabuwar damuwa ta cika masa zuciya.  “Yanzu wannan na nufin za a fasa kashin da ke goshi na kenan?”  ya tambaye ni watarana muna cikin hira.  Sai muka fashe da dariya.  Muka ce masa ai ko za a fasa, to ba za ka sani ba.  Wannan bawan Allah dai bai samu natsuwa ba. Da yaje ya kama tambaya kan irin wannan lalura, sai wasu suka ce masa ai wane da wane ma an musu irin wannan tiyata, amma basu kai labari ba; sun sheka barzahu.

Da muka ga dai damuwa ta kai masa ko ina, kasancewar abokinmu ne, a ma’aikata daya muke aiki, sai muka fara bashi shawaran cewa ya rage damuwa, idan kuwa ba haka ba, to, wata sabuwar cuta za ta kama shi.  Haka aka yi.  Cikin taimakon Ubangiji aka shirya masa takardun fita waje, aka masa biza zuwa kasar Indiya, muka masa addu’a, ya haye jirgi; sai kasar Hindu.  Kwanaki biyu da masa tiyata aka sallame shi.  Sai kwatsam ga Malam Sani ya dawo.  Kowa na tunanin ya ji an ce sai bayan mako daya zai dawo.  Yana zuwa sai ga shi garau, yana murmushi, babu ko bandeji a saman goshi ko idanunsa.  Babban Magana!  Ba a yi aikin bane? Ya ce an yi, “Ni kaina ban san da me suka yi ba. Kuma ko tsaga jiki na ba a yi ba.”  Daga nan na fahimci sabuwar fasahar tiyatar da suka yi amfani da ita.  Wannan fasahar tiyata ita ake kira “Laser Surgery” a fannin likitancin zamani; wato tsarin amfani da hasken Laser wajen yin tiyata.  Masu karatu, yau kuma ga mu dauke da bayani kan wata fasahar sadarwa a tsari da yanayin tururin haske ko iska mai dauke da sinadarai, mai kuma taimakawa wajen sawwake tsarin aiwatar da tiyata a wannan zamani namu.

Asali da Samuwa

Da farko dai, wannan fasaha ta hasken leza (wato Laser Light, ko Laser Beam, a turancin kimiyyar lantarki), tana samuwa ne ta amfani da tsarin kambama tururin haske ko iska zuwa yanayin haske mai kaifi, mai kuma tafiya a tafarki daya kacal.  Ana amfani da wannan kambamammen haske ne ta hanyar na’urar da ake kira leza a halin yanzu.  Na’ura ce mai dauke da kafofi guda biyu. Da kafar shigar sarrafaffen iska ko hasken, da kuma kafar da ke fitarwa.  Wannan kafa da ke fitar da wannan sarrafaffen haske ‘yar karama ce ainun, don haka hasken ke zama siriri.  Na’urar na fitar da hasken ne a yanayi daban-daban; akwai nau’in haske mai dauke da iska, akwai haske zalla mai dauke da launuka daban-daban.  Sannan na’urar tana da gejin kadadar zafi ko maimaituwar tsarin launi ko zafin da ake son wannan sarrafaffen iska ya fito da  su don a aiwatar da irin aikin da ake son yi.

Wannan ke nuna mana abubuwa guda hudu da ke tattare da wannan nau’in haske. Abu na farko, shi haske ne sarrafaffe daga sinadaran iska ko tururin haske (wato Radiation).  Abu na biyu shi ne, hasken na taskance ne a na’urar leza (mai yanayin girma da daban-daban).  Abu na uku shi ne, hasken na fita ne da karfi, da haske, da gwargwadon zafin da ake so, kuma hasken mai kaifi.  Abu na hudu shi ne, hasken na tafiya ne  a tafarki guda daya, ba ya barbazuwa. Bincike ya tabbatar da cewa nau’ukan hasken leza suna yanke abubuwa ne kamar yadda duk wani abu mai kaifi ke yankewa.  Ba ma nan kadai ba, suna da tasirin hasko wuraren da hannu ko almakashin mai tiyata ba za su iya shiga ba.

Wannan fasaha dai ta samo asali ne cikin shekarar 1960, lokacin da aka gudanar da bincike, aka tsara yadda fasahar za ta yi aiki, a rubuce.  A cikin shekarar 1974 ne aka kirkiri na’urar farko mai amfani da hasken leza.  Wannan na’ura kuwa ita ce na’urar manna tambari a jikin hajojin kasuwanci, wato Bar Code Machine.  A cikin 1978 kuma aka kirkiri na’urar faifan garmaho, wato Gramophone Player kenan. Na tabbata mai karatu ya san wannan na’ura.  To, tana amfani ne da nau’in hasken leza wajen haska layukan bayanai masu dauke da kide-kiden da ke cikin faifan.  Ana shiga shekarar 1982 kuma sai aka kirkiri na’urar CD, wato CD Player; wacce har yanzu muke amfani da ita wajen sauraro ko kallon fina-finan faifan CD.  Dagan an kuma sai kamfanin kera kwamfuta suka cafke, inda aka kirkiri na’urar dabba’a bayanai mai amfani da hasken leza ita ma.  Wannan na’ura ita ake kira Laser Printer, kuma har yanzu ana amfani da su wajen dabba’a bayanai.

- Adv -

Tun bayyanar wannan hikimar ta sarrafa haske don amfanin al’umma, an samu fannonin rayuwa da dama da suke amfani da ita wajen kere-kere, da yanke-yanke, da huje-huje, ko jone-jone.  Wannan kafin samuwar haka a fannin likitanci kenan.  Misali, manyan masana’antun kere-kere na amfani da wannan fasaha wajen yin waldan karafa.  Bangaren soji kuma na amfani da shi wajen gano inda abokan gaba suke a lokacin yaki, da darkake abokan gaba. A fannin tsaro ma ana amfani da wannan tsari na fasahar leza.  Da shi jami’an tsaro ke amfani wajen gano tambarin yatsun masu laifi, da tsarin gano masu laifi ta hanyoyin kimiyyar sadarwa na zamani.  A fannin binciken kimiyyar sararin samaniya ma akwai tsarin fasahar leza.  Galibin masu binciken kimiyya a halin yanzu na kan habbaka wannan fasaha ne don yin amfani da ita wajen tafasa sinadaran Yuraniyon, wanda makamashi ne mai muhimmanci wajen kera makamin nukiliya.

Sannan malaman kimiyya a jami’o’i suna amfani da fasahar hasken leza wajen gudanar da bincike ta hanyoyi da dama.  Idan muka koma bangaren bukukuwa da shakatawa, nan ma akwai hannun wannan fasaha wajen kayatar da jama’a. A kan yi amfani da wannan haske cikin yanayi mai ban sha’awa, a kawata wuraren biki da shi.  A halin yanzu da masu bincike suka fara tunanin hanyoyin sawwake matsalolin da ake fuskantan cikin tsarin tiyata a asibitoci, sai tunannin wannan fasaha ta hasken leza ta fado musu.

Amfani da Hasken Leza a Fannin Likitanci

Kamar yadda bayanai suka gabata, akwai fannonin rayuwa da dama da ake amfani da wannan fasaha mai matukar tasiri.  A dukkan fannonin nan kuwa, ana amfani da fasahar ne a irin yanayin da ya kamaci abin da ake son samarwa ko kawarwa ko gyattawa.  A fannin likitanci ana amfani da wannan fasaha wajen yin tiyata a saman fatar fuska da sauran bangaren jiki, kan abin da ya shafi cututtukan fata ko wani abin da ke makale a jikin fatar.  Wannan fanni shi ake kira Laser Skin Surgery.  Bayan shi, akwai kwararru kan fannin likitanci masu lura yin wannan aiki (wato Dermatologists), tare da amfani da wannan fanni har wa yau wajen gyaran fatan jiki don ado, wato Cosmetic Laser Surgery kenan.

A kan yi amfani kuma da wannan fasaha wajen gyaran hakora; masu kogo ne, ko masu girgidi, ko kuma namar da ke rike da hakora.  Sannan akwai tiyatar koda da ake yi da wannan fasaha ta hasken leza, wato Laser Kidney Stone Surgery kenanWannan shi ake amfani da shi wajen narkar da tsakuwan da ke cikin koda, ko duk wani dunkulalle ko daskararren abin da ya toshe hanyoyinsa.

Bayan haka, a kan yi amfani da hasken leza wajen aiwatar da tiyata a cikin idanu.  Wannan ma shi ne fannin da ya fi shahara a bangaren likitanci.  Shi yake sawwake aiwatar da tiyata cikin idanu ba tare da wasu matsaloli ba.  Akwai kuma tallafin da wannan fasaha ta hasken leza ke bayarwa wajen goge zanen haihuwa da ake wa mutane (wato Birth marks), da zane-zanen jiki irin na zamani da galibin turawa ke yi a yanzu, wato Tattoos.  A takaice dai, wanann fasaha ta hasken leza na taimakawa matuka wajen sawwake da yawa cikin matsalolin da ake fuskanta a bangaren tiyata a bangarorin jiki irinsu kunnuwa, da idanu, da fatan jiki, da koda, da dai sauransu.  Duk wata kafa ta jiki da ke lungu sosai, wacce sai an wahala kafin a kai inda take, duk ana iya riskarta ta amfani da wannan haske na leza.

Wannan haske na leza ya sha bamban da sauran haske da muka saba mu’amala da su a rayuwarmu ta yau da kullum.  Sauran nau’ukan haske sukan bazu ne da zarar sun fito daga muhallinsu.  Wannan tsari shi ake kira Light Scattering.  Kamar yadda hasken rana ke bazuwa, ta game dukkan ilahirin wurin da take haskawa.  Amma hasken leza ya sha bamban.  Wannan nau’in haske yana tafiya ne a tafarki guda daya tilo. Misali, idan kofar fitarsa kamar kofar allura ce, da zarar ya fito, a wannan yanayin na sirantaka da kaifi zai ci gaba da tafiya, har sai ya isa zuwa inda aka cilla shi, ba tare da karfin hasken, da kaifinsa, da sirantakarsa sun ragu ba.

Bayan haka, kowane haske yana zuwa ne da iya karfin iska ko zafin da aka yi gejinsa kafin fitowarsa, kuma idan ya fito, duk iya nisan tafiyar da zai yi, wannan gwargwadon zafi ba zai ragu ba. Wannan ke bashi tasirin shiga lungu-lungu, sako-sako, don baiwa mai mu’amala da shi damar gani ko taba nama, ko jijiya, ko wani yadin da ke karkashin fatan jikin dan adam. Akwai yanayin da ke fitar da haske kai tsaye, don kona wata fata ko yanke ta.  Akwai wanda ke fito da ballin haske (wato Light Pulses), akwai kuma mai fitowa a launuka daban-daban.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.