Tsarin Babbar Manhajar Android (8)

Kashi na takwas kuma na karshe, cikin jerin kasidun dake nazari kan babbar manhajar Android.

390

Dabaru da Kayan Aikin Ginawa

Bayan littattafai da kwarewa da kuma manhajoji, mai karatu na bukatar abubuwa guda uku mahimmai kafin ya gwanance wajen tsarawa da gina ingantattun manhajojin Android.  Idan bamu mance darasin makon jiya ba, mun yi bayani ne kan matakan ilimi ko kwarewa da a halin yanzu ake bi wajen gina wadannan manhajoji.  Tare da nuna cewa matakin karatu da kwatanta abin da aka karanta a aikace, su ne manyan tubali wajen gwanancewa a wannan sana’a.  A wannan mako za mu karkare wannan doguwar kasida ce da bibiyar hanyoyi uku na karshe, don cinma burin mai buri a wannan fage.

Sadaukar da Lokaci

Dayan biyu ne; ko dai ya zama ka dauki wannan fage ne don sha’awa kawai (hobby), don ka rika gina manhajoji kana amfani dasu ko raba wa mutane suna amfani dasu, ko kuma ya zama kana son daukan wannan fage ne a masayin sana’a.  Zai iya yiwuwa kuma kana son farawa da matakin farko ne, daga baya, iya gwargwadon yadda ka ga ka kware, ka nausa zuwa mataki na biyu.  Ko ma dai mene ne, dole sai ka sadaukar da kanka wajen wannan aiki.  Domin fannin gina manhajar kwamfuta (Programming) ba fannin ‘yan kailula bane; ayi yau, ba za a sake dawowa ba sai bayan wata ko watanni.   Idan ka fara karatu (a aji ne ko ta hanyar littattafai), dole ne ka ciyar da lokacinka a kowane lokaci; dare da rana safe da yamma.   Karatu ne da ya shafi karantawa da kwatantawa.  Duk abin da ka karanta, to dole ne ka kwatanta shi, don ilimin da fasahar da hikimar su tabbata a kwakwalwarka.  Hakan kuwa bazai yiwu ta dadi ba sai ka sadaukar da kanka.

Da yawa cikin masu karatu sun sha turo mini tambayoyi cewa wasu hanyoyi za su bi wajen koyon ilimin gina manhajar kwamfuta?  Wato “Computer Programming” kenan.  Ga wadanda na samu damar basu amsa, nakan shawarce su da su tanadi lokaci ne, a karon farko.  Domin sai ka baiwa karatu lokacinka, sannan zai baka kansa, ka kwashi abin da kake so.  Amma idan dabi’arka ita ce kailula, ka je ka nemi wani fannin daban ba wannan ba.  Wannan ita ce gaskiya mai daci da ta kamata mai karatu ya santa, ya fahimce ta, sannan ya hakikance samuwarta don cin nasara.

Hakuri da Juriya

Bayan bayar da lokaci, dole ne mai karatu kuma ya dimanci hakuri da juriya.  Meye bambancin dake tsakaninsu?  Shi hakuri shi ne tilasta rai ko zuciya wajen yin abin da ba lalai bane taso a kowane lokaci, don samar mata da maslaha a kusa ko a nesa.  Kada mai karatu ya damu dani, wannan ma’anar da na bayar a al’adance nake nufi.  A daya bangaren kuma, juriya shi ne: tabbatuwa akan hakuri.  Wato ka jure dabi’ar hakuri; jiya, da yau, da gobe, da jibi…ilaa maa shaa’Allahu.  Domin kana iya yin hakuri na minti biyar, ko goma, ko sa’o’i, kai ko ma shekara.  Amma daga baya kayi zarya saboda gazawa.  Wannan ba lalai bane ya samar maka da maslahar da kake so cikakke.  Amma ka dimanci hakuri, ka daure a kan hakuri, ka kuma jure, shi ne abin da ake kira: Juriya.

Ga wanda ya dabi’antu da dabi’ar hakuri da juriya, kwarewa a fannin gina manhajar Android ba wani abu bane mai wahala.  Domin sinadarin aikin kenan. A farkon lamari za ka ta tafka kura-kurai masu yawa, masu muni.  Idan ba ka da hakuri sai ka fasa ma baki daya.  Sannan kana iya kashe lokaci mai tsawo kana tsara wata manhaja, sai ka fara ginawa a aikace, ka zo gwaji, sai ka cije.  Kana iya daukan kusan mako baka fahimci a ina matsalar take ba.  Idan ba ka da hakuri sai ka fasa.  Amma idan ka jure, kana cikin bincike sai ka ga ma ashe watakila wani digo ne kawai ka mance baka diga a gaban wata kalma ba.  Kana digawa shikenan, sai ka ga manhajar ta mike, rau rau, zam zam.

Bayan ka gama ginawa ma tsuguno bata kare ba.  Kai, yanzu ne ma ka fara aikin.  Sai ka dauki tsawon lokaci kana gwaji (Test Running), kana gano kurakurai (Debugging), sannan kana gyara inda aka samu matsaloli.  Kuma abinka da wayoyin salula, duk da cewa babbar manhajar iri daya ce, amma dole sai ka ta gwaji a wayoyin kamfanoni nau’uka daban-daban, don tabbatar da daidaituwarta a kowane irin mahalli (Stability and Compatibility).  In kuwa ba haka ba, sai aiki ya dawo danye, bayan a tunaninka komai daidai yake.  Dukkan wannan na bukatar hakuri da juriya.  Da zarar ka tanadi wadannan sinadaran rayuwa guda biyu, sai abu na karshe, wato: kayan aiki.

- Adv -

Kayan Aikin Ginawa

Kayayyakin aikin da kake bukata sun kai biyar zuwa shida.  Abu na farko dai shi ne, dole ka mallaki kwamfuta, nau’in tafi-da-gidanka (Laptop) ko ta kan tebur (Desktop), wacce za ka iya jona ta da Intanet lokaci zuwa lokaci.  Sannan dole ne ya zama tana dauke da manhajar da za ta iya riskar da kai zuwa Intanet, wato Manhajar Lilo kenan (Internet Browser).  Amfanin mallakar kwamfuta kuwa shi ne, duk abin da za ka gabatar a kanta zai gudana; daga farko har karshe.  Sannan dukkan manhajojin da za ka yi amfani dasu wajen wannan aiki, daga Intanet za ka saukar dasu.  Wani abin sha’awa ma shi ne, dukkan wadannan manhajoji da tsare-tsare kyauta ne, ba za ka kashe ko kwandala ba.

Bayan mallakar kwamfuta da karikitanta, sai manhajoji guda hudu da za ka saukar, daga gidajen yanar sadarwa daban-daban.  Kamar yadda na fada a baya ne, dukkan wadannan manhajoji kyauta ake bayar dasu.

Manhajar farko ita ce manhajar JAVA.  Za ka samu wannan manhaja mai dauke da tubalin gina manhajar kwamfuta da yaren Java ne a http://java.oracle.com/downloads.   Duk da cewa zubin Java a halin yanzu yana kan na takwas ne (Version 8 – Java 1.8), har yanzu ba a fara gina manhajar Android da zubin Java na bakwai ma ba, sosai, balle na takwas.  Idan kaje za ka saukar da zubin Java na shida ne (Java 6, ko Java 1.6).  Bayan haka, akwai nau’uka wajen uku ne – Java Runtime Environment, da Java EE, da Java SE.  Sai ka saukar da Java SE, wato “Standard Edition” kenan.  Bayan ka gama saukarwa sai ka loda (Install) wa kwamfutarka.

Manhaja ta biyu ita ce manhajar “Android SDK,” wato tubalin dake dauke da tsare-tsaren gina manhajar Android.  Cibiyar aikin kenan, gaba daya.  Wannan za ka same ta a gidan yanar sadarwar Android, kai tsaye.  Sai ka saukar, amma bayan ka gama saukarwa (Downloading), ba loda (Install) wa kwamfutarka za ka yi ba, domin ba dunkulalliyar manhaja bace irin ta al’ada.  Za ka nemi mahalli ne a ma’adanar kwamfutarka (Drive C:), sai ka bude sabon burgamin adana bayanai (Folder), ka adana a ciki.  Idan ba canza mata suna aka yi ba, za ka ga sunan kamar haka: android-sdk-windows.  Da zarar ka adana wannan tubali a mahallinsa, sai ka zarce Intanet don neman makami na uku, wato allon rubutu kenan.

Manhaja ta uku ita ce allon rubutu, wato “Text Editor.”  Akwai nau’ukansu da yawa.  Amma wanda yafi shahara, yafi sauki, sannan yafi dacewa da tubalin Java SE da ka saukar a fari, shi ne: Eclipse Text Editor, wanda ke dauke da abubuwa da dama masu sawwake aikin.  Babban aikin wannan allon rubutu, kamar yadda mai karatu zai ga shafinsa a tsakiya, a kansa ne maginin manhajar zai ta tsara yadda yake son manhajar ta kasance, a rubuce.  Bayan ya rubuta, yayi gwaji, sannan yayi ‘yan gyare-gyaren da suka kamata, akwai kwarangwal na wayar salula nau’uka daban-daban a jikin wannan allo, wadanda mai karatu zai rika amfani dasu wajen gwaji.  Wadannan kwarangwal su ake kira “Mobile Emulator.”  Duk abin da ka gina, sai ka kira wannan kwarangwal na wayar salula, ka loda manhajar a ciki, za ta nuna maka yadda manhajarka za ta bayyana a hakikanin wayar salula.  Amma kafin ka kai ga wannan mataki na fara gina manhaja, sai ka saukar da makami na karshe.

Wannan makami kuwa ba wata manhaja bace mai zaman kanta, a a.  Karin tagomashi ne, wato “Plugins.”  Da zarar ka loda wa kwamfutarka wancan manhaja ta allon rubutu mai suna: “Eclipse Text Editor,” sai ka budo wannan allo, kaje sashen “Windows” dake sama ka matsa, sai ka gangara can kasa, ka latsa: “Android SDK Manager,” nan take zai fara saukar maka da wadannan bayanan tagomashi.  Wadannan bayanai ana kiransu “Eclipse Android Plugins” ne.  Aikinsu kuwa shi ne su tabbatar kana gina manhajar da ta dace da babbar manhajar Android dake dauke kan wayoyi ne.

Idan mai karatu bai mance ba, a baya munyi bayani kan nau’in zubin Android, wato “Android Versions.”  Wadannan nau’uka sun sha bamban, tunda ba lokaci daya aka gina su ba. Don haka, wannan dan aike mai suna “Android SDK Manager” shi zai saukar maka da dukkan bayanan da suka dace da kowane irin nau’in Android ne.  Domin da zarar ka yi yunkurin kirkirar sunan manhajar, tun kafin ka kai ga samar da sassanta, za a bukaci ka tantance nau’in Android din da kake son Manhajar da kake ginawa ta dace da ita.  Sai dai kuma, idan kana saukar da wadannan bayanai, dole ne ka tanadi “Data” mai dimbin yawa, domin yana daukan lokaci, duk da cewa ya danganci nau’in bayanan da kake bukatar saukarwa.  Da zarar ka gama saukarwa kuma, sai ka kama aiki.

Kammalawa

Wadannan, a takaice, su ne iya abin da zan iya samarwa ga masu karatu kan batun babbar manhajar Android.  Nan da makonni uku masu zuwa, in Allah ya yarda, akwai kasidar da za ta bibiyi wannan wajen dacewar maudu’i, mai take: “Korafe-Korafen Jama’a kan Android.”  Ita ce kasidar da za ta fayyace wa mai karatu dalilan da suka sa yake korafi kan dabi’u da halayyar Android.  Kafin nan, za mu sauya akala don gudanar da bincike na musamman mai take: “Manyan Tekunan Duniya: Tsarinsu, da Abubuwan dake Dauke Cikinsu,” a mako mai zuwa, in Allah yaso.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.