Waiwaye Kan Darussan Baya (2)

Duk tafiyar da aka kawata ta da waiwaye, to akwai watakilancin samun nasara cikinta, in Allah Ya yarda.  Da wannan muka ga dacewar ci gaba da wannan salo na “Waiwaye Adon Tafiya”, a wannan shafi mai albarka.  Idan masu karatu basu mance ba, wannan shi ne karo na biyu da muka sake zama don yin nazari kan kasidun da suka gabata, kafin mu sake canza salon tafiya don ci gaba.  A wancan karo mun yi waiwaye ne saboda ganin mun samu bayanai kan yadda ake sarrafa shafukan yanan gizo, da kuma tarihin da ke tattare da asalinsa.  Wannan shi ne daman abin da ya kamata mai koyo ya sani.  Hakan kuma ya faru ne a mako na bakwai da fara assasa wannan shafi.  A yau sai ga mu a mako na ashirin da takwas!  Tirkashi!  Don haka naga dacewar mu sake zama don kallon baya; ina muka fito?  A ina muke?  Kuma ina muka dosa?

91

Tuna Baya Shi ne Roko

————————————————-

Kasidun Baya

Bayan gabatar da “Waiwaye Adon Tafiya” kashin farko, mun ci gaba ne da kasidar Matambayi Ba Ya Bata, ko Search Engine, a takaice.  In da muka sanar da mai karatu hanyoyin da zasu taimaka masa nemo bayanai a giza-gizan sadarwa ta duniya.  Daga nan sai muka sake sanar da masu karatu wasu daga cikin shugabannin da ke tafiyar da al’amura a duniyar Intanet.  Wannan ya samu ne ta hanyar Shugabanni a Duniyar Intanet, wacce makalar Kwamfuta da Manhajojinta ta biyo baya.  A makon da ya biyo wannan, sai muka kawo wasu tambayoyi guda biyu da masu karatu suka turo; daya kan Sakonnin Bogi ne, wato Spam Mails, sai kuma wanda ke neman bayani kan VoIP, ko kuma Voice Over Internet Protocol, a turance.  Bayan dukkan wannan, sai muka jefo kasidu biyu – daya na bin daya – kan alakar Hausawa da Intanet, da kuma hanyoyin da Intanet zai iya shafan al’ummar Hausawa nan gaba.  Daga nan kuma sai kasidar da tafi dukkan sauran shahara ta biyo baya, wato Fasahar Intanet a Wayar Salula.  Akwai watakilancin ba za mu kawo kashi na biyunsa ba, sabanin yadda na fara tunani kafin wannan mako.  Zan yi Karin bayani nan gaba.  Ana cikin haka, sai muka ga dacewar fahimtar da mai karatu ire-iren hanyoyin da zai iya mu’amala da wasu kamfanoni ko hukumomin gwamnati ta hanyar Intanet, ba tare da yaje can inda ofishin hukumar yake ba.  Wannan makala mun kacalcala ta ne zuwa kashi biyar, muka ba ta taken: Dangantakar Intanet Da Harkokin Rayuwa. 

Idan mai karatu bai mance ba, muna cikin barko wadannan bayanai ne muka dan yi ratsi, don jefo bayanai gamsassu kan yadda ake iya ragewa ko kuma rabuwa da sakinnin bogi.  Taken wannan kasida kuwa itace: “Spam”: Don Kawar da Bakin Haure.  Daga nan muka zarce taska don nemo ma mai karatu bayanai kan tarihi da habbaka da kuma yadda ake gina Mudawwanar taskance ra’ayoyi da tunani a giza-gizan sadarwa ta Intanet.  Mudawwana (Weblog) #1, shi ne taken kasidar farko.  Daga nan muka biyo kasidar makon da ke biye da wannan da kashi na biyu, wato Mudawwana (Weblog) #2.  A bayyane yake cewa, bayan kasidar Fasahar Intanet a Wayar Salula, ba a samu kasidun da suka shahara, suka kuma yi tasiri a zukata da gabobin masu karatu ba irin wadannan.  Abin da ya dada tabbatar mana da hakan kuwa shi ne, bayan sakonnin text da muka yi ta samu, da dama cikin masu karatu sun bude mudawwanai, wanda duk mun yi ta sanar da adireshin su a wannan shafi.  Bayan haka, sai kuma muka fara zuwa ziyara takanas-ta-gizo, zuwa wasu daga cikin shahararrun gidajen yanar sadarwa masu muhimmanci ga al’umman Hausawa, a duniyar gizo.  Mun fara ne da gidan yanan sadarwar Gamji.com.  Daga nan muka biyo da na Kanoonline.com.  A karshe muka yi zango a kasar Amurka, daidai gidan Malam Mohammad Hashim Gumel, mai gidan yanar sadarwan Gumel.com.  Alal hakika mun karu sosai da wannan ziyara, domin a kalla mun san irin matsayin da wadannan gidajen yanar sadarwa suke dashi, da kuma irin bayanan da suke dauke dasu.  Da kuma uwa-uba, irin tsarin da Uban Gidan Yanar yayi musu, don amfanar da masu ziyara.

To, gama wannan ziyara ke da wuya, sai ga wani abu a kan matan Sarki, wanda saboda rashin kula, ba ido ba, ta kasa gani.  Af, mun dade muna ta kwararo bayanai kan yadda ake shiga da kuma mu’amala da fasahar Intanet, amma bamu taba kawo bayani kan masarrafa  ko manhajar da ke taimaka ma mai ziyara wannan aiki ba.  Don haka sai muka jero kasidu biyu kan Rariyar Lilo da Tsallake-tsallake (Web Browser).  A makalar farko muka kawo asali da kuma tarihin wannan manhaja mai muhimmanci a tarihin fasahar Intanet.  A kasida ta biyu, wacce muka kawo cikin makon da ya gabata, sai muka kawo siffofin shahararriyar rariyar kamfanin Microsoft, wato Internet Explorer 6.0.  Da wannan makala muka cike wannan zango na wannan lokaci.  Idan mai karatu ya lura, zai ga cewa karantarwan wadannan kasidu da bayanansu suka gabata, sun sha banban nesa ba kusa ba, daga tsarin kasidun farko.

Sakonnin Masu Karatu

Duk da yake kusan dukkan mako mukan tabo daya ko biyu, a kalla, dangane da abin da ya shafi sakonnin masu karatu, a yau ya kamata mu yi kyakkyawan nazari kan irin abin da masu karatu ke rubutawa sakamakon kasidun da wannan shafi ke fitarwa, ta gwargwadon tunani da hangen nesan su.  Ire-iren wadannan sakonni sun kasu kashi uku ne, dangane da nau’in bayanan da ke cikinsu.  Kashi na farko sun kunshi sakonni ne na gaisuwa da yabo da kuma ban gajiya.  Ina samun irin wadannan sakonni ta hanyar sakon text na wayar salula ko kuma ta Imel.   Kashi na biyu kuma sun kunshi sakonnin neman Karin bayani kan abin da na rubuta a makon da ake ciki ko kuma wanda ya gabata.  Sai kuma kashi na karshe, masu bayar da shawarwari kan abin da ya kamata a yi.  Ga al’ada na kan mayar da jawabi ne kai tsaye, idan aiki bai rinjayeni ba.

Wasu lokuta kuma ire-iren wadannan sakonni kan sameni ne (musamman ta hanyar text), a halin rashin kudi a cikin wayata. Idan na sanya wasu lokuta sai in kira, ko in mayar da jawabi, wasu lokuta kuma in shagala. Akwai wasu sakonni wadanda sun kunshi tambayoyi ne, ban kuma bayar da amsarsu ba don ganin cewa nan ba da dadewa ba za mu kawo bayanai kan haka.  Don haka duk wanda ya rubuto don neman Karin bayani, amma bai samu amsa ba har yanzu, ya gafarceni. In Allah Ya yarda nan ba dadewa ba zai samu cikakken bayanai nan gaba.  Muna bin abin ne daki-daki.  Wanda kuma ya rubuto gaisuwa ko shawara shi ma bai ji wani bayani ba, don Allah yayi hakuri shi ma; komai da lokacinsa.

- Adv -

Maimaitattun Tambayoyi

Kafin mu karkare, zan so sanar da masu karatu cewa akwai wasu bangarori biyu da har yanzu da dama cikinmu bamu samu gamsuwa da su ba.  ko dai saboda watakil bamu fara bin wannan shafi tun farko ba, ko kuma saboda irin takaitattun bayanan da ke cikinsa.  Kada a mance, wannan shafi ne na jarida, wanda ba za mu iya kawo komai da komai a lokaci guda ta yadda kowa da kowa zai fahimta ko iya amfani da abin da ake karantarwa ba.  Wannan ba abu bane mai yiwuwa a tsarin yau da kullum, da kuma tsarin tarbiyya irin ta karantarwa.  Don haka maimaitattun tambayoyin neman Karin bayani ko shiryarwa da suka fi kowanne zuwa su ne kan Yadda ake shiga Intanet ta Wayar Salula, da kuma bayani kan yadda ake shiga shi kanshi Intanet din, a farkon al’amari.  Kari a kan haka, wasu kan rubuto don neman Karin bayani kan wani littafi da zai taimaka musu wajen shiga Intanet.   Wannan tasa na kebe wannan bangare don amsa wadannan tambayoyi, a karon karshe, in Allah Ya yarda.  Ga bayanan nan kasa:

Intanet a Wayar Salula

Ga duk wanda ke biye da wannan shafi mako zuwa mako, ya san wannan na daga cikin kasidun da masu karatu suka fi damuwa dashi.  Kuma a iya kokarin da nayi wajen bincike kan kasidan da na gabatar, nake ganin kamar idan muka kawo kashi na biyu, za a samu cakudewar fahimta, domin dukkan abin da ya kamata a ce na kawo dangane da shiga Intanet ta hanyar Wayar Salula, to na kawo shi.  Abubuwan da suka rage kuma maimai ne kan na baya.  Na kuma fahimci galibin masu neman bayani (ba Karin bayani ba) kan haka, da cewa basu samu karanta wannan makala bane.  In kuma sun karanta, to dama basu fahimci matakan da aka kawo ba.  Don haka nake baiwa ire-iren wadannan makaranta da su je Mudawwanar wannan shafi don samun kasidar kai tsaye a nan: http://fasahar-intanet.blogspot.com/2007/05/fasahar-intanet-wayar-saluala.html .  A lura da adireshin, a kuma shigar dashi yadda yake a nan.  Za a samu cikakken bayani in Allah Ya yarda.

Yadda ake Shiga Intanet

To, wannan kusan ita ce kasida ta biyu ko uku da muka gabatar a wannan shafi.  Idan muka ce za mu sake koro bayani kan haka kuma, kamar mun koma baya ne.  Don haka na ke son sanar da duk mai neman bayani kan haka da yaje Mashakatar Tsallake-tsallake (cyber café) da ke gari ko unguwar su, ya sanar da su cewa so yake ya bude Imel (kada y ace musu Intanet kawai zai shiga).  Bayan haka, yana da kyau ya sanar dasu cewa bai taba shiga wannan muhalli ba, ko kuma a kalla bai saba mu’amala da kwamfuta ba.  Su zasu koya masa yadda zai shiga, bayan sun bude masa akwatin Imel.  Idan ma yai sa’a, to tare zasu bude; suna gaya masa yadda zai yi, shi kuma yana yi. . . har dai ya bude.  Da zarar ya gama, nan zai fahimci cewa abin ba wani wahala bane dashi.  Don haka sai ya lazimci zuwa a kullum.  Ko kuma a kalla sau biyu a mako.  Hakan ne zai sa ya samu kyakkyawar kwarewa kan wannan fasaha, in Allah Ya yarda.

Dangane da abin da ya shafi littafi kan Intanet kuma, mun sanar a wannan shafi cewa akwai littafi amma ana kan masa gyara ne tukunna, kafin fitowarsa.  Kuma da zarar ya fito za a sanar a nan.  Duk da cewa akwai littafai yan kanana da aka rubuta cikin harshen turanci, idan mai karatu yai sa’a ya same su, sai ya fara dasu.  Don haka sai a ci gaba da hakuri; komai da lokacinsa.

Kammalawa

Daga karshe, a mako mai zuwa za mu juya akala zuwa wasu bangarori kuma, don fadada sanayyarmu ga wannan fasaha.  Sai a biyo mu don samun cikakkun bayanai.  A kuma rika kwatanta abin da aka koya idan  wanda ya shafi aikatawa ne a aikace.  Domin wannan na daga cikin hanyoyi mafi muhimmanci wajen tabbatar da ilimi a kwakwalwar dan Adam.  Ina mika godiya ta ga dukkan masu rubuto sakonni ta dukkan hanyoyi; da wanda na rubuto masa amsa ko na kira shi, da wanda ban kira ko bashi amsa ba, duk ina godiya.  A rika hakuri da ni, dan Adam nake; ba dukkan komai bane zan iya yi a lokaci guda.

Kafin in karkare, ina mika godiya ta musamman ga Dakta Yusuf Adamu da ke Jami’ar Bayero a Kano.  Mun gode da irin karfafa guiwa da yake wa wannan shafi a duk mako.  Daga karshe ina mika godiyata ga kowa da kowa; ka rubuto ko ba ka rubuto ba!  Allah hada fuskokinmu da alheri, amin.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.