Waiwaye Kan Darussan Baya (6)

Wadanda suka saba karanta wannan shafi tun farkon farawa sun san cewa a duk karshen zango, mukan zauna don yin waiwaye, abin da Malam Bahaushe ke kira “Adon tafiya.”  A yanzu shekarun wannan shafi namu shida kenan da watanni shida cif-cif.  Kuma wannan shi ne zama na shida da za mu yi, don yin bitar darussan da muka yi ta kwasa a baya.  Ga wadanda basu san wannan tsari da shafin ke gudanuwa a kai ba, shafin Kimiyya da Kere-kere ya samo asali ne cikin watan Oktoba na shekarar 2006; farkon taken shafin shi ne: Kimiyya da Fasaha.  Mun kuma yi waiwaye karo na daya, da na biyu, da na uku ne a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008.  Zama na karshe da muka yi, wanda shi ne waiwaye na hudu, ya zo ne cikin watan Satumba na shekarar 2008, daidai lokacin da shafin ya cika shekaru biyu kenan.  Ga shi mun sake dawowa a yau don yin nazari kan kasidun baya, a karo na shida, kamar yadda masu karatu za su gani daga taken kasidar.

175

Tuna Baya….

A yau ma za mu yi nazari ne kan darussan da muka koya a wannan zango.  Zama na karshe mun yi shi ne cikin watan Mayu na shekarar da ta gabata. Bayan haka, za mu ga yawan kasidun da muka kawo a zangon, da abin da suke karantarwa, da irin usulubin da muke bi wajen tafiyar da shafin, da tsarin mu’amala da masu karatu, da kasidun da ba a gama su ba, sannan mu ji inda za mu dosa a zangon da ke tafe.

Me Muka Koya Daga Darussan Baya?

Da farko dai, wannan shafi ya faro ne da kasidu kan fasahar Intanet da sadarwa zalla.  Daga baya ne muka sauya wa shafin take daga: Kimiyya da Fasaha zuwa Kimiyya da Kere-kere.  Wannan sauyin take ya samo asali ne sanadiyyar sauyin nau’ukan fannonin da shafin ke magana a kai.  Daga fasahar Intanet da wayar salula zuwa sauran fannonin kimiyya da kere-kere, da sararin samaniya, da sinadarai, da halittar jikin dan adam, da kuma fannonin dabi’u da zamantakewa.  Ya zuwa makon da ya gabata, mun gabatar da kasidu guda 256 kan dukkan wadancan fannoni.  Idan muka hada da kasidar wannan mako, sun zama 257 kenan.  A waiwaye adon tafiya na farko muna da kasidu 7.  A zango na biyu muna da kasidu 22.  A zango na uku muna da kasidu 17.  A zango na hudu muna da kasidu 33.  A zango na biyar muna da kasidu guda 132. Sai zango na shida, wanda muke bitarsa a yau kenan, muna da kasidu guda 46, har da wannan kenan. Idan ka kebe wannan zango, dukkan kasidun sauran zangunan suna nan daram!  Zan fadi dalilin rashin kammaluwan kasidun wannan zango nan gaba.

Kamar yadda bayani ya gabata a sama, a wannan zango mun gabatar da kasidu kan nau’ukan ilimi daban-daban.  Zangon ya bude ne da kasida kan Mazan Jiya, inda bayani ya zo kan shahararren Malami Ibn Al-Haitham, daya daga cikin manyan malaman musulunci da suka shahara a fagen ilimin kimiyya a karnonin baya.  Sai kasida kan samuwar haruffan Hausa masu lankwasa a kwamfutocin zamani, mai taken: Akwai Haruffan Hausa cikin Kwamfutocin Zamani.  Daga nan kuma muka faro shahararriyar silsila kan yadda matasanmu ke gudanar da rayuwarsu a dandalin abota ta Intanet mai suna Facebook.  Taken kasidar shi ne: Rayuwar Matasanmu a Dandalin Facebook.  Mun kuma gabatar da kasidu biyar a wannan bangare, kuma za mu ci gaba.  Daga nan kuma sai shafin ya kutsa fagen ilimin kimiyyar sinadaran halitta, wato Molecular Biology, inda muka faro silsila mai take: Tsarin Gadon Dabi’u da Siffofin Halitta.  A nan ma mun gabatar da kasidu har shida, za mu kuma ci gaba in Allah ya so.  Don har yanzu ko rabin bayanan bamu kawo ba.

Daga cikin kasidun wannan zango har wa yau akwai mai taken: Tsarin Mu’amala da Wayar Salula, wanda ci gaba ne cikin jerin kasidun da muke kawowa a wannan fage, da irin ci gaban da ake samu lokaci-lokaci.  Wannan kasida da wannan take ta dauki tsawon makonni 12.  Wannan ya faru ne sanadiyyar tafiya da nayi na kusan watanni biyu a shekarar da ta gabata.  Bayan na dawo kuma sai muka kwashe makonni kamar uku muna amsa tambayoyi, tare da tsokaci ko gyaran da masu karatu suka aiko mana.  Gama wannan ke da wuya sai ga kasidu hudu a jere, masu taken: Dandatsanci: Sabon Salon Yaki a Tsakanin Kasashen Duniya.  Idan mai karatu ya samu karanta wannan kasidu duka, ba zai yi mamaki kan dambarwar da ke faruwa tsakanin kasar Amurka da wasu kasashe ba cikin wannan mako, kan batun tsohon ma’aikacin hukumar CIA mai suna Snowden.  Idan dambarwar ta ci gaba, watakila mu kawo kasida guda daya don amfanin mai karatu.

Daga nan kuma sai kasida ta musamman kan bacci a mahangar kimiyya, mai taken: Samuwar Bacci da Mafarki a Mahangar Kimiyya.  A wannan fage mun kawo kasidu guda uku ne rak, amma batun bai kare ba.  Domin bayanan sun tsaya ne kan bacci kadai, bamu tabo batun mafarki ba. Don haka da sauran rina a kaba.  Kada in mance, kungiyar Tsangayar Alheri da ke Dandalin abota ta Intanet ta gayyace ni zuwa babban taronta na shekara-shekara da aka yi a katsina cikin watan Janairun wannan shekara.  Na kuma halarta, tare da gabatar da kasida daya mai shafuka 11.  Wannan kasida mai take: Rayuwar Matasa a Dandalin Abota ta Intanet, an buga ta a wannan shafi har na tsawon makonni biyu.  Sai kuma kasida mai take: Ku Inganta Mana Makarantun Kimiyya da Kere-kere, wanda muka samu makonni uku muna kawowa, amma Allah bai kaddari mun gama ba.  Sauran kasida guda daya, wacce za ta cike sauran bayanan da suka gabata.  Wadannan su ne wadanda zan iya kawowa cikin kasidun da suka gabata.

Ina Muka Dosa?

A zangon gaba in Allah ya so, akwai ci gaban wasu kasidun, da kuma kawo wasu sababbi, masu tsawo ko matsakaita.  Daga cikin wadanda za mu ci gaba dasu akwai Bayani Kan Wayar Salula, wanda ya zuwa yau bayanan sun kai shafuka 83.  Sannan za mu ci gaba da bayanai kan Tsarin Gadon Dabi’u da Siffofin Halitta (Genetics), da bayanai kan Rayuwar Matasa a Dandalin Facebook, sai kuma karashen kasidarmu mai taken: Samuwar Bacci da Mafarki a Kimiyyance, tare da kasidar: Ku Inganta Mana Makarantun Kimiyya da Kere-kere.  A baya ma akwai kasidun da ke bi na bashi, kamar kasidar: Samuwar Ruwa da Sinadaran da ke Cikinta, ba mu karasa ta ba, da kuma kasida mai taken: Makamashi da Dukkan Nau’ukansa, shi ma bamu gama shi ba.

- Adv -

Bayan wadannan, in Allah yaso akwai sababbin kasidu a fannin kere-kere.  Za mu kawo bayanai kan tasirin kimiyyar fasahar bayanai ga fannin kere-kere.  Wannan kasida za ta dubi yadda fannin kera motoci a duniya ke amfani da masarrafan kwamfuta wajen inganta hajojinsa.  Sannan za mu kawo bayanai na musamman kan babban titin dogo na zamani da ke birnin Dubai, wato Dubai Metro Train Track; yadda aka gina shi, da tsarin kiran jiragen, da makamashin da suke amfani dashi wajen diban jama’a daga zango zuwa zango.  Dadi na nesa, wai Ungulu ta hango masai. Sai kuma bincike kan tasirin kimiyyar sadarwa ga zamantakewar jama’a a duniya baki daya.

Mu’amala da Masu Karatu

A wannan zango ma kamar sauran zangunan da suka gabata, masu karatu sun rubuto tambayoyi, wasu na amsa su nan take, wasu kuma na buga su, wasu kuma, wadanda maimaitattu ne, ban saurare su ba.  Sannan akwai wadanda suka bugo waya don nuna gamsuwa, ko don godiya ko kuma neman karin bayani kan kasidar da suka karanta a makon, nakan saurare su, duk da cewa nace ba a kira sai dai a rubuto tes.  Dan adam ajizi ne.  Akwai kuma wadanda suka rubuto don bukatar kasidun baya, su ma nakan aika musu.  Wasu in aika musu nan take, wasu kuma sai bayan wani lokaci. Ya dai danganci halin da na samu kaina sadda suka aiko bukatarsu.

Har wa yau a cikin wannan zango na samu sakonnin gyara sosai daga wajen masu karatu.  Shahararre daga cikinsu shi ne wanda na samu daga Malam Auwal Yakubu, wani masanin fannin kimiyyar sararin samaniya.  Na kuma buga a wannan shafi, ina kuma mika godiyata a gare shi matuka. Allah saka masa da alheri.  Akwai wadanda suka aiko mini da sakonni kan wani abin da suka ga na rubuta wanda bai musu daidai ba, ba don cewa abin da na fada ne bai yi daidai ba; nakan musu karin bayani, kuma sukan ce kada a buga a shafin jarida, kuma ban buga ba.  A iya zato na, da wanda ya min gyara yace a buga don jama’a su gani (tunda a baya sun ga kuskure na), da wanda yace kada a buga, a dai gyara, duk na dauka sun yi hakan ne don Allah, don kuma neman gyara, kuma Allah ya saka musu da alheri baki daya, amin.

Bayan haka, akwai wadanda ke daukan lambar wayar da suka gani a shafin, su yi ta min filashin.  Idan na kira sai a ce kawai a jarida aka gani.  To, na dai sha bayani kan ladubban kiran waya, da kuma cewa idan ba ka da kudi a wayarka da zai wadatar da kai kira, kayi tes, in babu na tes, ka hakura ko kaje inda ake buga waya na kudi ka kira.  Hakan ya fi mutunci. Yin filashin idan ba ga wanda ya sanka ya kuma san lambarka ba, kuskure ne matuka, sai in ya zama tsananin lalura.  Don Allah mu kiyaye.

Bayan haka, na san masu karatu sun ga canjin yanayi a wannan shafi, ma’ana wasu lokuta a kan ji ni shiru babu abin karatu a shafin.  Wannan ya faru ne sanadiyyar kalubalen rayuwa da nai ta cin karo dasu a wannan zango.  Ba korafi nake ba, sai don bayani.  Wannan kalubale ne yayi tasiri matuka kan rayuwata, ciki har da rubutun da nake yi a wannan shafi.  Don haka a gafarce ni, in Allah ya yarda al’amura za su daidaita nan kusa.  Wannan ne ma yasa nace kasidun wannan zango basu kammala ba, ma’ana akwai wadanda idan aka bukace su daga gare ni ba za a same su ba.  Wannan ya faru ne sanadiyyar rasa kwamfuta ta da nayi, kamar yadda bayani ya gabata a baya.  Amma wani abin farin ciki kuma shi ne, duk kasidar da aka bukata a waje na ba a samu ba, za a samu a shafin Mudawwanarmu dake: http://fasahar-intanet.blogspot.com, da kuma http://kimiyyah.blogspot.com. Sai a garzaya.

Kammalawa

A karshe dai, ina mika godiyata ga dukkan masu karatu; tsakanin masu bugo waya, da masu rubuto tes, da wadanda ma ba a jin duriyarsu, wanda su ne suka fi yawa.  Allah saka wa kowa da alheri.  Ina mika godiyata ga Editan Aminiya Malam Bello Muhammad, da irin gudunmawar da yake bani, tare da hakuri da ni sanadiyyar halin da na samu kaina.  Sai godiya ga Malam Abubakar AbdurRahman (Dodo) da Malam Ahmad Garba, masu lura da wannan shafi nawa. Ina godiya gare su matuka, musaman wajen shawarwari da suke bani kan yadda zan inganta  shafin baki daya.  Sannan ina godiya ga kamfanin Media Trust, tare da mika ta’aziyya ta ga hukumar kamfanin kan rasuwar Manejin Edita, Malam Suleiman Muhammad.  Allah gafarta masa, ya sa Aljanna ce makomarsa, ya kuma kyautata namu karshen.

Hakika na san Malam Suleiman sosai tun shekarar 1998, yana cikin mutanen da suka yi tasiri matuka a rayuwata kan harkar rubutu.  Allah gafarta masa.  Sannan kuma shafin Kimiyya da Kere-kere na mika godiyarsa ga Sashen Hausa na BBC da irin sanayyar da suke baiwa shafin wajen gayyata na ofishinsu, da yin hira da ni kan al’amuran da ke faruwa a fannonin kimiyyar sadarwa musamman, da kuma amsa tambayoyin masu sauraronsu.  Su ma a wannan zango sun gayyace ni kusan sau goma zuwa ofishinsu da ke nan Abuja. Ina godiya matuka, musamman ga Babban Edita Malam Bashir Sa’ad Abdullahi, da sauran ma’aikatansu irinsu: Ibrahim Mijinyawa, da Raliya Zubairu, da Naziru Minka’ilu, da sauransu.

Jama’a, zan dakata a nan, sai Allah ya hada mu a mako mai zuwa.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.