Yadda Aka Gina Manhaja da Shafukan Facebook (2)

Ga kashi na biyu cikin jerin kasidun dake mana bayanin tsari da yadda aka gina manhaja da shafukan Dandalin Facebook. A sha karatu lafiya.

210

Da Me Aka Gina Shafukan Facebook?

Kafin bayani kan da me aka gina shafukan dandalin facebook da muke mu’amala dasu a kullum; ko dai ta wayoyin salularmu, ko ta shafukan kwamfutarmu, zai dace mu fahimci irin nauyi da wannan dandali ke dauke dashi.  Wannan ne zai taimaka mana wajen fahimtar dalilan da suka sa hukumar facebook suke amfani da irin masarrafai ko kayan aiki da ba kowane irin gidan yanar sadarwa bane ke dauke dasu; a bayyane ne ko a boye, wadanda ba ma iya ganinsu da idanunmu.

Bayanai sun gabata cewa a halin yanzu dandalin facebook na dauke ne da mutane miliyan dubu daya da dari biyu, wato biliyan daya da miliyan dari biyu kenan (1,200,000,000).  Wannan dimbin jama’a na lilo ne a kan wannan dandali a kullum.  A yayin da ake samun masu shiga wannan shafi ta amfani da kwamfuta, kusan kashi 50 na shiga ne ta wayoyin salularsu, ko ta na’urorin sarrafa bayanai irin su iPad, da Samsung Galaxy Note ko Tab, da Google Nexus da dai sauran ire-irensu.  Wannan ke nuna irin girma, da sarkakiya da kuma tarin “kwazo” da wannan dandali ke da shi, musamman wajen karban sakon bukatun jama’a (User Requests) a kullum.

Shekaru 4 da suka gabata, sadda mambobin wannan dandali basu shige miliyan 800 ba, an kiyasta cewa a kowane dakika guda (second), dandalin facebook na samun bukatun jama’a sama da miliyan 15! – tsakanin masu kokarin shiga (log in), da masu kokarin fita (sign out), da masu budo hotuna, da masu lodawa, da masu zuba sakonni (posts), da masu nemansu don karantawa, da masu aika bukatar abota ga wasu (friend requests), da masu amsa bukatar abota, da masu loda wakoki, da masu nemansu don karantawa, da masu budo shafukan wasu don sanin tarihinsu, da masu rubuta tarihinsu a shafukansu, da masu yin rajista a farkon lokaci, da masu rufe shafukansu saboda wasu dalilai, da masu leken asiri kan wasu, da masu turo wa wasu sakonni ta manhajar sako (Message), da masu karanta sakonnin da wasu suka aiko musu.  A kowane dakika, ire-iren wadannan abubuwa ne ke faruwa a wannan dandali.

Ga duk mutumin da ya san tsarin sadarwa ta kwamfuta, da yadda kwamfuta ke aika sako, da yadda take karbar sakon mai neman sako daga gare ta idan Uwar Garke ce (Web Server), ya san wannan ba karamin aiki bane. Sannan ba kowace irin kwamfuta bace za ta iya gabatar da ire-iren wadannan ayyuka a wannan zamani.  In kuwa haka ne, to da wasu irin kwamfutoci ne Hukumar Dandalin facebook ke amfani dasu wajen aiwatar da wannan aiki gagarumi?

Rothschild, daya daga cikin jami’an hukumar Facebook ya ce wannan dandali na facebook na ajiye kwamfutocinsa ne a manyan biranen kasar Amurka guda uku. Birnin farko shi ne birnin San Franciso, birni na biyu Santa Clara, sai birni na uku, wato Virginia.  Yace hukumar Facebook na amfani ne kwamfutoci masu dauke da babbar manhajar Linux, masu dauke da masarrafar Uwar Garke (Server) na manhajar Linux, wato Linux Servers kenan a turance.  Wadannan kwamfutoci dai kowannensu na dauke ne da na’urar sarrafa bayanai da ake kira Processor, guda takwas!  Tirkashi.  Wani aikin sai mai shi.   A yayin da kwamfutar zamanin yau na dauke ne da na’urar sarrafa bayanai guda daya, ko biyu, ko hudu, idan abu yayi zafi.   Ba nan aka tsaya ba, Roth yace a kalla suna da irin wannan kwamfuta mai aikin aikawa da karbar bukatun masu mu’amala da dandalin facebook sama da guda 800!  Su ne a warwatse a wadannan birane, dauke da bayanan jama’a.   Mizanin wadannan kwamfutoci ya kai terabyte 40 (40 terabytes), wato Gigabyte biliyan 40 kenan.  Wannan mizanin babbar ma’adana kenan, wato Hard Disk Drive.  Ma’adanar wucin-gadinsu kuma, wato RAM, ya kai terabyte 15, ko kace Gigabyte biliyan 15 kenan.  Wannan ma’adana na wucin-gadi ne ke dauke da shafukan da aka fi bukata, wadanda da zarar an tashi sake bukatarsu, a wannan ma’adana ake dauko su, ba sai an koma can cikin babbar ma’adana ba, don kauce wa tsaiko.

Dandalin facebook na dauke ne da wani tsari mai ban mamaki, mai ban al’ajabi, mai kayatarwa, amma ga wanda ya san tsarin sadarwar zamani da yadda yake aiki a yau.  Amma ga wanda bai sani ba, sai an masa kwatance mai saukin saukakewa, mai saukin fahimta.  Muna iya fahimtar wannan sarkakiya ne daga irin alkaluman bayanai da ke fitowa daga masana kan yadda wannan dandali ke aiki.

- Adv -

Kari a kan alkaluman da suka gabata a baya, masana sun tabbatar da cewa a duk cikin minti 20, masu mu’amala a wannan shafi na aikawa ko loda hotuna miliyan biyu da dubu dari bakwai da goma sha shida (2,716,000).  A duk cikin cikin minti 20 sukan yada (share) rariyar likau (web links) guda miliyan daya (1,000,000).  A duk minti 20 sukan makala sunayen abokansu kan hotunansu sau miliyan daya da dubu dari uku da ashirin da uku (1,323,000).  A duk cikin minti 20 na duniya, sukan rubutu sakonni a bangon shafinsu guda miliyan daya da dubu dari biyar da tamanin da bakwai (1,587,000).  A duk cikin minti 20 sukan fadi wani abu a shafinsu (status update) sau miliyan daya da dubu dari takwas da hamsin da daya (1,851,000).  A duk minti 20, masu karatu su kara sani, akan samu amsa bukatar neman abota (Friend Requests accept) guda miliyan daya da dubu dari tara da saba’in da biyu (1,972,000).  A duk minti 20 a dandalin facebook, ya kai mai karatu ka kara sani, ana samun ta’aliki kan rubutun wani (comments) guda miliyan goma da dubu dari biyu da takwas (10,208,000).   Sannan an tabbatar da cewa a duk minti 20 din nan dai har wa yau, masu mu’amala a shafin facebook na aikawa da sakonnin bayan fage (Private Messages ko Messages) guda miliyan hudu da dubu dari shida da talatin da biyu (4,632,000)!  Dankari!

Uku daga cikin manyan kalubale da ke fuskantar hukumar gudanarwar dandalin facebook dai su ne: dandazon sarkakiyar da ke cikin bukatar bayanai daga masu mu’amala a shafin a kowane dakika guda, da tarin yawan bayanai da ke taruwa tuli-tuli, a duk dakika guda (ciki har da wannan sako da kake karantawa), da kuma sarkakiyar da suke fuskanta wajen jera bayanai ta la’akari da mahimmancinsu wajen masu bukata a kowane lokaci.

Kada mai karatu ya rikice.  Duk da wannan sarkakiya da yake jin ina ambato, abin mai sauki ne a misalin yau da kullum.  Na yi bayani a baya cewa dandalin facebook na dauke da manyan bangarori uku ne.  Akwai bangaren farko, wanda shi ne kamar idon-gari; in da duk masu mu’amala da shafin ke mu’amala da shi.  Wannan bangare ne ke karbar sakonka –  na bukatar neman aboki, ko neman wani shafi, ko tura sakon ta’aliki, ko wata bukata dai a takaice  – kuma shi ne mai maido maka da jawabi – kan abin da ka bukata!  Wannan a fili kenan; abin da kuma kake gani kenan.  Amma ba shi ne mai hakikanin aikin ba.  Shi dan sako ne.  Wannan bangare shi suke kira “Front-End” a turancin kimiyyar sadarwa na zamani.

Sai bangare na uku, wanda ke dauke da dukkan bayanan da muke mu’amala da dasu a makare.  Wannan bangare shi ne bangaren ma’adanar kwamfuta mai dauke da babbar manhajar taskance bayanai da aka fi sani da “Database Servers” a turance.  Wannan bangare ne ke rike da dukkan bayanan da suka shafi dukkan masu shafi a dandalin facebook, a ajiye.  A turancin kimiyyar sadarwar zamani ana kiran wannan bangare da suna: “Back-End,” ko bayan gida.

Sai bangare na biyu wanda ke tsakanin bangaren farko da bangare na uku.  Aikin wannan bangare shi ne kwafo shafukan da masu mu’amala da dandalin facebook suka fi bukata a dukkan lokuta.  Idan ka shiga shafinka a karon farko, wannan bangare zai taskance shafin a ma’adanarsa.  Da zarar ka sake shiga shafinka sai wannan bangare ya gano cewa ai ka shigo dazu, kuma akwai makwafin shafin da ka bukata a baya, sai kawai ya baka shafin nan take, ba sai ya koma asalin ma’adanar da ke bangare na biyu da bayaninsa ya gabata ba.  Wannan bangare shi ake kira “Caching System.”  Amfanin samar da wannan bangare shi ne don rage saibi ko nawa wajen dauko bayanan da ka bukata dake makare a wancan ma’adana dake bayan fage, ko “Back-End.”   Watakila sai na kawo misali da tsarin banki sannan mai karatu zai fahimta.

A tsarin banki, idan ka kawo musu kudi ajiya, za a karba a jiye a taskar bankin, wanda ke babban bankin Najeriya.  Idan ka bukata ma za a je babban banki ne a dauko kudin, sai a biya ka.  To amma ganin cewa kafin a je a dauko maka wani ma yazo bukata, wanda hakan zai kawo tsaiko wajen kaikomo tsakanin bankinka da babban bankin Najeriya, sai kawai aka samar da wata ‘yar karamar ma’adana ta wucin-gadi a cikin bankin.  Wannan ma’adana ita ake kira “Strong Room.”  Maimakon ace duk sadda ka bukaci kudinka aje babban bankin Najeriya a dauko a biya ka, sai aje cikin wannan ma’adana ta “Strong Room” a dauko wadanda aka karba na wasu, a baka.  Idan kuma har lokacin tashi yayi ba a samu masu bukatar karba ba, sai a koma dasu taskar bankin da ke babban bankin Najeriya.  To haka tsarin karba da mika bayanai yake a dandalin facebook.

Kada mai karatu dai ya mance cewa muna kan bayani ne kan: “Da wani irin kayan aiki aka gina shafukan dandalin facebook?”  Wannan shi ne abin da ke tafe a kasida ta gaba in Allah yaso.

- Adv -

You might also like
Leave A Reply

Your email address will not be published.