Yadda Na’urar ATM Ke Aiki (2)

Bangaren karshe, wanda kuma dole ne a same shi kafin aiwatar da mu’amala da wannan na’ura ta ATM ya yiwu, shi ne katin da ake tsofa shi a cikin na’urar, don sanar da ita bukatun da ake da su.  Idan babu wannan kati ba za a iya yin komai da wannan na’ura ba.  Wannan kati dai shi ne katin ATM, ko “ATM Card” a harshen Turanci.  Kati ne na soyayyen roba (wato Plastic), wanda ke dauke da sinadaran hango bayanai boyayyu, wato Micro-chip a cikinsa.  Kati ne da banki ke bayarwa don aiwatar da cinikayya ko cire kudi ta hanyar wannan na’ura ta ATM, kamar yadda muka sani.  Wannan kati na ATM yana dauke ne da bayanai nau’uka hudu a cikinsa.

 

Bayanan farko su ne bayanan da suka danganci bankin da kake ajiya dashi, ko bankin da ya ba ka katin a takaice. Wadannan bayanai su ake kira “Routing Number”, kuma su ne bayanan da ke nuna wa na’urar ATM din kake son mu’amala da ita cewa ga bankin da kake ajiya dashi nan.  Kuma su ne bayanan da masarrafar gudanarwa (wato Host Processor) ke amfani da su wajen gano bankin da kake ajiya da su, don samun saukin biyan bankin da ka ciri kudi daga na’urar ATM dinsu, idan ba na bankin da kake ajiya da su bane.  Misali, idan kana ajiya a bankin Fidelity ne, kuma kayi amfani da katin da suka baka na ATM wajen ciro wasu kudade daga taskar ajiyarka ta hanyar na’urar ATM din bankin Zenith, da wadannan bayanai na Routing Number ne masarrafar gudanarwar za ta gano asalin bankinka.  Sai nau’in bayanai na biyu, wato lambar katin da aka ba ka, kamar lambar takardar cak kenan.  Wannan su ake kira “Serial Number”. Nau’in bayanai na uku kuma su ne lambar taskar ajiyarka ta banki, wato “Account Number,” shi ma yana cikin wannan kati.  Shi kuma zai taimaka ne wajen baiwa na’urar damar “magana” da kwamfutocin bankinka don gano yawan kudin da kake da shi a taskar.

 

Idan kudaden sun kai yadda za ka iya dibawa, sai kwamfutocin su baiwa babbar masarrafar gudanarwa dama, ita kuma ta sanar da na’urar don ba ka daman cire yawan abin da kake bukata. Idan abin da ka bukata bai kai yawan abin da ka mallaka ba, sai a ce wa na’urar ta hana ka dibawa.  Dukkan wannan sadarwa na faruwa ne cikin kasa da dakiku biyar zuwa goma, a harshen tsarin sadarwa ta kwamfuta. Sai nau’in bayanai na hudu da ke cikin katin, wato lambobin sirri, ko “Personal Identification Number” (PIN).  Lambobi ne guda hudu da za a ba ka tare da katin, za kuma a gaya maka cewa ka canza su zuwa lambobin da kake bukata kuma za ka iya tuna su cikin sauki.  Da zarar ka sa katin a cikin na’urar, akwai inda aka rubuta “Change PIN”, idan ka matsa za a kaika inda za ka canza su zuwa lambobin da kake so. Wadannan lambobi su ne kalmomin shiga wannan na’ura.  Idan ka mance su ko ka batar da su, to, ba za ka iya mu’amala da ita ba, sai ka koma bankinka sun ba ka wani.  Dukkan wadannan bayanai nau’uka hudu suna dauke ne cikin wannan kati na ATM da ake bayarwa.  Sai a kiyaye.

 

Tsarin Gudawarwa

Tsarin mu’amala da na’urar ATM ba abu bane da yake da fuska daya tinkwal.  Akwai bangarori guda hudu da ake bukatar samuwansu kafin aiwayar da cinikayya – na cire kudi ne, ko duba balas, ko kuma wasu nau’ukan kasuwanci da ake iya yi ta hanyar na’urar. Bangaren farko shi ne samuwar katin ATM din, tare da mai katin, wanda zai sarrafa na’urar kenan.  Bangare na biyu kuma shi ne samuwan na’urar ATM din da kanta, wacce za a tsofa katin a ciki don aiwatar da sadarwa.  Bangare na uku shi ne babban masarrafar gudanarwa, wato Host Processor, ko kuma kamfanin da ke mallakar wannan masarrafa, wato InterSwitch kenan a Najeriya.  Domin shi ne kamfanin da ke da wannan babbar masarrafa a Najeriya. Duk da cewa akwai wasu kamfanoni kanana, amma galibin bankunan Najeriya na amfani da babbar masarrafar gudanarwarsa ne.  Sai bangare na karshe, wato bankin da mai katin ATM ke ajiya da shi, ko kuma bankin da ya bayar da katin.  Wadannan su ne bangarori hudu da ake bukata kafin a iya sarrafa wannan na’ura don cire kudi ko neman balas ko sayan katin waya ko biyan kudin wutar lantarki ko na ruwa, a Najeriya.

 

Da zarar ka zo inda na’urar ATM take girke, za ka same ta ne cikin “yanayin hutu,” wato “Standby Mode,” muddin ba wani bane a wajen yana amfani da ita.  Kana iya gane haka ne idan ka ji sautin tallace-tallace na tashi daga gare ta.  Ko kuma ka ga an rubuta “Insert Your Smart Card” ko makamancin hakan.  Amma idan ka ga an rubuta “Service Not Available” ko kuma “Service to be Available Shortly”, to ba ta cikin yanayin da za ka iya sarrafa ta ka samu biyan bukata.  Wannan sako na nuna cewa ana zuba wa na’urar kudade kenan. Sai kawai ka nemi wata na’urar.  Amma idan ka same ta tana ta tallace-tallace, sai ka tsofa katinka a ciki.  Da zarar katin ya shiga, za ta kalli katin da kyau, ta karanta sakonnin da ke cikinsa.  Daga nan sai a yi maka “barka da zuwa” (in har wacce ke magana ce), sai a ce maka ka “Shigar da kalmomin shiganka”, wato PIN Cord kenan, kamar yadda bayanai suka gabata a baya.  Lambobi ne guda hudu wadanda kai kadai ka sansu.  Da zarar ka shigar, in daidai ka shigar, sai na’urar ta budo maka abubuwan da za ka iya gudanarwa.  Idan kudi kake son cirewa, sai ka matsa inda aka rubuta “Cash Withdrawal.”  Da zarar ka matsa, sai a budo maka inda za ka zabi yawan kudaden da kake son cirewa – dubu 10, ko 20, ko 40, ko 5, ko 2, ko 1.  Da zarar ka matsa abin da kake son cirewa za ta sake maka wasu tambayoyi – kana son rasit ne?  Sannan idan ba ATM din bankin da kake ajiye da su bane, za a sanar da kai cewa za a cire naira dari daga cikin taskar ajiyarka, ka amince?  Idan ka ce eh, sai ta zarce.

 

Abu na gaba da na’urar za ta yi shi ne, sai ta mika wadannan bayanai da ka shigar zuwa ga babbar masarrafar gudanarwa na kamfanin Interswitch misali, wato Host Processor kenan.  Wannan masarrafa ce za ta tuntubi kwamfutar da ke dauke da bayanan taskar ajiyarka, a bankin da kake ajiya.  Da zarar ta sanar da kwamfutar cewa ga abin da kake bukatar cirewa, sai kwamfutar ta yi nazarin abin da ke cikin taskarka, idan basu wuce yawan abin da ke ciki ba, sai nan take ta sanar da babbar masarrafar gudanarwar cewa “A ba shi daman cire abin da yake bukatar cirewa.”  Daga nan sai wannan babbar masarrafa ta cire adadin wannan kudi da kake son cirewa daga taskar ajiyarka zuwa taskar kamfanin Interswitch, sai kuma ta sanar da na’urar ATM din da kake tsaye a gabanta kake jira, cewa ta baka daman cire abin da kake son cirewa na kudi.  Nan take sai ka ji na’urar ta fara wata ‘yar kara daga kafar da ke cillo kudade (wato Cash Dispenser), tana kirgo maka su kenan.  Idan ta gama kirgo su, sai ta cillo maka su.  Kana kwashewa sai ta tambaye ka: shin kana son gudanar da wasu ayyuka ne?  Idan ka ce a a, sai a cillo maka katinka.   Idan na’urar da ka cire kudi daga gare ta na bankin da kake ajiya da su ne, to wannan ba matsala.  Domin kai tsaye ne kawai.

 

Amma idan na wani banki ne daban, lokacin da babbar masarrafar gudanarwa ta samu bayanai daga kwamfutar bankin da kake ajiya da su, sai ta aiwatar da abin da ake kira Electronic Fund Transfer; ma’ana ta “karbo” wannan adadin kudi da kake son cirewa daga taskar ajiyarka ta banki, ta adana su a taskarta.  Sai ta umarci na’urar ATM din da kake tsaye gabanta kake jira, da ta cillo maka iya adadin kudin da kake bukata.  Abin da ya faru a nan shi ne, ka cire kudin daga cikin kudaden wani banki ne da ba naka ba, amma kuma tuni an cire iya wannan adadi daga taskar ajiyarka, don biyan wannan banki da ka ciri kudin ta hanyar na’urarsu.  Da zarar gari ya waye, kamfanin Interswitch zai biya wannan banki da ka cire kudi daga na’urarsu.  A nan sun zama kamar dillalai kenan tsakaninka da wani banki.  Naira dari da ake cirewa daga taskarka a duk sadda kake cire kudi daga wata na’urar da ba na bankinka ba, la’ada ce ko ladan hidimar da aka maka ne. Wannan ita ce hanyar da ake bi a biya duk bankin da wani ya cire kudi ta hanyar na’urar ATM dinsa, wanda ba kwastoman bankin bane.  Wannan ke nuna saukin mu’amalar da ke tattare da wannan tsari na mu’amalar kudi.  Domin duk inda ka je da katinka kana iya cire kudi, hatta a wasu kasashe.  Kamar bankin GTBank misali, idan kana rike da katinsu ka je wata kasa, kana iya cire kudi daga taskar ajiyarka, amma daloli ne za ka cire ba naira ba.  Kuma duk sadda ka cire wani abu, bankin zai caje ka naira dubu daya kudin Najeriya.

 

Wasu Kalubale

Duk abin da ya shafi mu’amala da tsarin sadarwa ta zamani, duk da sauki da ingancin tsarinsa, sai ka samu wasu ‘yan matsaloli duk kankantansu kuwa.  To balle kuma Najeriya.  A farkon bayyanan wannan sabuwar tsarin mu’amala da kudi an samu matsaloli da dama.  Amma galibinsu masu alaka da zamba ne, kuma mun tattauna kansu a kasidun da muka gabatar shekaru biyu da suka gabata.  A halin yanzu akwai matsaloli da ke faruwa lokaci-lokaci masu alaka da tsarin sadarwa.  Daga cikinsu akwai matsalar makalewar kati bayan ka cire abin da kake son cirewa ko kafin ka cire.  Sai katin ya makale ya ki fitowa.  Idan haka ta faru da kai kada gabanka ya fadi.  Idan na’urar bankin da kake ajiya da su ne, ka shiga ciki in lokacin aiki ne, ka musu bayani.  Za a hada ka wani jami’a da zai zo ya bude don ciro maka katinka.  Idan kuma na wani banki ne, bayan ka sanar da su, sai dai ka jira, domin za su kaiwa bankinka ne, ba za su baka hannu-da-hannu ba.  Wannan shi ne tsarin.

 

Wasu lokuta kuma kana iya sanya katin, ka sanar da na’urar iya kudin da kake son cirewa, sai ta dade tana ce maka ka jira, amma a karshe kuma ta cillo maka katinka ba tare da ta turo maka kudi ba.  Amma kana tsaye a wurin kuma sai ka ji sakon tes ya shigo cewa “Ka cire naira kaza daga taskar ajiyarka, saura naira kaza da kaza.”  Babu abin da ya fi wannan tayar da hankali. To duk kada ka damu.  Wasu bankuna a halin yanzu sukan aiko wani tes nan take bayan wancan, mai nuna cewa an mayar maka da kudinka cikin taskar ajiyarka nan take.  Na sha samun haka da bankin Fidelity kuma nan take suke juya tsarin.  Idan bankinka bai aiko maka da tes da ke nuna an mayar maka da kudinka ba, sai ka kai musu rasitin da na’urar ta baka.  Idan kaje za a ce ka rubuta wasika zuwa ga Manajan bankin, duk kada ka damu, sai ka rubuta – ka ambaci yawan kudin, da ranar, da wurin da kaje cirewa, da lokacin.  Daga nan za su yi amfani da wancan kundi da na’urar ke taskance bayanan dukkan mu’amalan da aka yi da ita, wato Journal Print Out.  A ciki za su samu bayanan yadda mu’amala ta kasance tsakaninka da na’urar, sai su mayar maka da kudinka.

 

Wasu lokuta kuma kana iya zuwa ka shigar da dukkan bayanan da ake bukata, sai a ce maka “Contact Your Financial Service Provider” haka na faruwa ne idan kudin da ke cikin taskar ajiyarka ba zai iya biyan abin da ka bukata ba a lokacin.  Misali, ka bukaci a baka dubu 10, alhali dubu 9 da dari biyar ne a taskarka.  Sannan kana iya ganin wannan sakon da ke cewa: “Financial Services not Available,” idan bankinka na da matsalar tsarin sadarwa.  Wannan ke nuna cewa babbar masarrafar gudanarwa ta kasa isa ga kwamfutocin da ke dauke da bayanan taskar ajiyarka nenan.  A wasu lokuta kuma kana iya zuwa na’urar ATM ka bukaci kudi sai a ce maka: “Unable to Dispense Cash.”  Abin da wannan sako ke nufi shi ne, babu kudi a cikin ma’adanar na’urar.  Don haka sai ka yi hakuri ka je wata na’urar daban.

 

Kammalawa

Wadannan, a takaice, su ne kadan cikin abin da zai iya samuwa dangane da yadda tsarin ATM Machine yake aiki.  Saura da me? Akwai da yawa cikin mutane wadanda basu yadda da wannan tsari na cire kudi a banki ba, saboda ire-iren matsalolin da ke faruwa musamman kan rashin tabbas.  Wannan ba wani abin mamaki bane. Abin da ke da muhimmanci mu sani shi ne, shi fa wannan tsari an samar da shi don baka damar cire kudi a lokacin da abin da ke hannunka ya kare, ko kuma wani lamari na gaggawa ya same ka da ke bukatar kashe kudi.  Amma kuskure ne mutum zai yi tafiya, sai ya ki cire kudi wai don yana takamar yana da wannan kati a hannnunsa.  Wannan bai kamata ba, domin bai kamata mutum ya gina hukunci kan abin da ba shi da tabbaci ba a kansa.  Tabbaci shi ne ka cire kudinka a lokacin da ka yanke hukuncin tafiya. Rashin tabbas shi ne ka jinkirta cire kudi don kawai akwai na’urar ATM a inda za ka je.  Wannan kuskure ne.

Baban Sadik

Baban Sadik marubuci ne, kuma mai bincike a fannin kimiyya da fasahar sadarwar zamani da tasirinsu ga al'umma a kasashen Afrika, musamman Najeriya. Ya tanadi wannan shafi ne don taskance dukkan kasidun da yake gabatarwa a shafinsa na jaridar AMINIYA mai take: "Kimiyya da Kere-kere," wanda ya faro tun shekarar 2006; shekaru goma kenan a takaice. Bayan kasidun shafin jarida, wannan shafi har wa yau yana dauke da wasu kasidun da ya gabatar a tarurruka da aka gayyace shi, ko wasu hirarraki da gidan rediyon BBC Hausa yayi dashi a lokuta daban-daban. Baban Sadik na zaune ne a birnin tarayyar Najeriya, wato Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *